Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta ce za’a kara wa’adin taimakawa kasar Girka

Majalisar wakilan kasar Jamus ta amince da karin wa’adin watanni hudu domin tallafawa tattalin arzikin kasar Girka da ke fama da matsalolin komadar tattalin arziki

Европейские лидеры на саммите в Брюсселе, 16 июля 2014.
Европейские лидеры на саммите в Брюсселе, 16 июля 2014. (©Reuters)
Talla

Karin wa’adin wanda cibiyoyin ba da Basussuka suka amince a makon jiya sannan ita kasar Girka ta aiwatar da gagarumin sauye-sauye, na bukatar kasashe masu amfani da kudaden Euro su amince da shi.

Wasu wakilan majalisar ta Jamus sun dan nuna shakkunsu game da yiwuwar tsarin, amma duk da haka an zartas da shi.

Wakilan majalisar kasar Jamus 542 ne suka jefa kuri’ar amincewa, yayin da wakilai 32 suka jefa kuri’ar kin amincewa, sannan wasu 13 suka ki jefa kuriar kwata-kwata.

Wannan mataki na zuwa ne bayan da a jiya Alhamis ’yan Sanda da masu zanga-zanga suka kaura fada a wajen wani gangamin da masu adawa da Gwamnatin Girka suka kira a birnin Athens.

Boren na jiya da aka yi a Athens, shi ne na farko a karkashin sabuwar Gwamnatin kasar, wata daya da ya gabata, wato sabuwar gwamnatin da ta yi alkawarin sake duba yarjejeniyar dimbin basussukan da ake bin kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.