Isa ga babban shafi

Faransa ta kama hanyar zama kasa ta farko da za ta halasta zubar da ciki

A yau Litinin ake sa ran ‘yan majalisar dokokin Faransa su amince da sanyar damar zubar da ciki a cikin kundin tsarin mulkin kasar, lamarin da ya samu gagarumin goyon baya a kasar.

Faransa za ta kasance kasa ta farko a duniya da ta amince da zubar da ciki idan majalisar dokokinta ta amince da kudirin dokar.
Faransa za ta kasance kasa ta farko a duniya da ta amince da zubar da ciki idan majalisar dokokinta ta amince da kudirin dokar. © AFP/Fadel Senna
Talla

A zaman kada kuri’ar da za a yi a yau da misalin karfe 2 da rabi agogon GMT, ana bukatar a samu rinjaye na 3 cikin biyar a dukkannin matakan majalisar, kafin wannan kudiri ya shiga kundin tsarin mulki.

Idan majalisar ta amince da wannan, Faransa za ta kasance kasa daya tilo a duniya da ke da dokar kare masu bukatar zubar da ciki a kundin tsarin mulkinta.

A shekarar da ta gabata, shugaban Faransa, Emanuel Macron ya sha alwashin tabbatar da halasta zubar da ciki a kasar, bayan da kotun kolin Amurka ta soke dokar, lamarin da ya sa wasu jihohi na kasar suka haramta zub da ciki.

A watan Janairu, majalisar wakilan Faransa ta amince da kudirin halasta zubar da ciki da gagarumar rinaye a wata kuri’ar da ta kada, inda yanzu ake jiran sahalewar majalisar dattawa.

Kuma ana sa ran kudirin dokar ya tsallake duk wata sarkakiya bayan kuri’ar da majalisun biyu za su kada a fadar Versailles in an jima a Litinin din nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.