Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta yi watsi da zargin kisan Ameniyawa

Kasar turkiya ta jaddada kin amincewar ta da daukan laifin kisan kare dankin da aka yi wa Ameniyawa a lokacin yakin duniya na farko shekaru 100 da suka wuce. Kasashen duniya dai na ta matsin lamba ga gwamnatin Turkiya da suke zargin ta da kisan kare danki ga Armeniya a lokacin yakin duniya na farko,

Tayyip Erdogan, Shugaban Kasar Turkiya.
Tayyip Erdogan, Shugaban Kasar Turkiya. REUTERS/Henry Romero
Talla

Dakarun daular Usmaniya sun fafata da daular Rasha, sai dai Turkiyan ta tsaya kan bakanta na cewa ba za ta karbi laifin da ake kokarin kakaba mata ba.

Kasar ta Turkiya ta jaddada rashin amincewar ta da karban laifin ne inda ta mayar da martani ga fafaroma Francis, shugaban mabiya darikar katolika ta duniya dangane da kalmar ‘kisan kare danki’ daya ke amfani da ita wajan siffanta aukuwar lamarin

Firaministan Kasar ta Turkiya Ahmed Davutoglu , a martanin da ya mayar wa fafaroman , ya caccake shi da cewa yana bin bayan bangare guda ne a lamarin, kuma ya kara da cewa bai nuna damuwar sa ba a kan halin da musulmai suka shiga a lokacin barkewar yakin duniyan na farko.

Gwamnatin Turkiyan dai ta bayyana cewa, dubban Turkawa da Armeniyawa ne suka rasa rayukansu a yakin da dakarun daular usamaniya suka fafata da daular Rasha da ta yi kokarin karbe ikon yankin Anatolia a wancan lokacin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.