Isa ga babban shafi
Turkiya

Kotun Turkiya ta hukunta Mutane 2 saboda batanci ga Shugaban Kasar

Kotun kasar Turkiyya ta ci wasu mutane biyu tara, bayan ta same su da laifin yin zanen batanci domin cin zarafin shugaban kasar Racep Tayyip Erdogon

Tayyip Erdogan, Shugaban Kasar Turkiya.
Tayyip Erdogan, Shugaban Kasar Turkiya. REUTERS/Osman Orsal
Talla

Mutanen biyu Ozer Aydogon da kuma Bahadir Baruter, gwanayen iya zane ne, da ke aiki a wata jaridar barkwanci mai suna Penguen.

A can baya kotun ta yanke masu hukuncin dauri na tsawon watanni 11, to amma a yanzu aka dawo da hukuncin a matsayin na biyan tara ta Euro dubu 2 da 700 kowanne.

A watan Agustan shekara bara ne, Jaridar barkwancin ta zana mutane biyu, tsaye a kofar shiga fadar shugaban kasar, inda su ke marhaba da shigowar Tayyip Erdogan a matsayin sabon Shugaban Kasa, bayan ya lashe zabe a watan na Agusta, kuma su ka yi masa gaisuwa ta wulakanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.