Isa ga babban shafi
Faransa

An gurfanar da Faransawa 4 akan cinikin Hodar Iblis a Dominica

A Jamhuriyyar Dominica an fara shari’ar Faransawa guda hudu da aka kama suna dauke da Buhun Hodar Iblis zuwa Faransa shekaru biyu da suka gabata a tashar jirgin kasa ta birnin Punta Cana

channel4.com
Talla

Faransawan sun kunshi matuka jirgi guda biyu da fasinjoji biyu wadanda ake zargin suna fataucin miyagun kwayoyi ta barauniyar hanya a jiragen sama.

A jiya Litinin ne Faransawan suka fara gurfana gaban kotun birnin Santo Domingo a Jamhuriyyar Dominican, tun lokacin da aka cafke su shekaru biyu da suka gabata.

Faransawan hudu kuma sun hada da matuka jirgi guda biyu da wasu mutane biyu wakilansu da ke fakewa da sunan fasinjoji, da aka kama kayansu makare da Hodar Ibilis.

An dade dai ana jiran a fara shari’ar Faransawan, wadanda ake zargi suna fatauci ta barauniya hanya a jirgin sama.

Amma kotu ta dage sauraren shari’ar har zuwa wani lokaci bayan masu gabatar da kara sun bukaci a dauke shari’ar zuwa wata Kotu.

A watan Maris din 2013 ne aka cafke mutanen a Tashar Jirgin Punta Cana, kuma mahukuntan kasar Jamhuriyar Dominica sun ce an cafke su ne, a lokacin da suke cikin shirin tashi a cikin wani karin jirgi da suka makare da Hodar ta Ibilis.

Yanzu kuma ana zargin Faransawan guda hudu tare da wasu jami’an tsaron kasar Dominican da suka taimaka masu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.