Isa ga babban shafi
Faransa

Kotu a Faransa ta aika Sammacin kama mutane 3 kan harin Rosiers

A cikin watan fabrairun da ya gabata ne, Kotu a kasar Faransa, ta gabatar da sammacin kasa-da-kasa domin kama wasu mutane 3 da ake zargi da kai harin ta’addanci a Unguwar Rosiers, ta yahudawa a birnin Paris a 1982

Talla

Harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6, kamar yadda majiyar Shara’a a kasar ta Faransa ta sanar bayan share tsawon shekaru 32 da faruwar lamarin.

Mutanen 3 da ake zargi na rayuwa ne a halin yanzu a gabar yamma kogin Jodan da kuma Kasar Norway, an kuma gano su ne a karkashin binciken da Alkali da ke kula da laifukan ta’addanci na birnin Faris Marc Trévidic ke gudanarwa.

A ranar 9 ga watan Agustan 1982 aka jefa makamin Gurneti a wani shagon shan Shayi da ke Unguwar Yahudawa ta Rosiers a birnin Paris, inda ya fashe a tsakkiyar taron jama’a sama da 50, kafin daga bisani mahara 2 su kutsa kai a shagon suka kuma buda wuta a kan jama’a.

Majiyar binciken ta ce mahara 3 zuwa 5 ne suka kai hare-haren, wadanda bayan aikata ta’asar, suka sulale tare da watsar da harsasan Bindigoginsu, kirar kasar Polongne a gefan hanya

Harin da aka kai a cikin minitana 3 ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 a yayinda wasu 22 suka jikkata,

tun a wacan lokaci ne dai aka zargi wani gungun palestinawa karkashin hukumar cin gashin kan palestinawa ta PLO, da kuma kungiyar Fata ta Abu Nidal wanda ya rasa ransa a 2002 a wani yanayi dake ci gaba da kasancewa a duhu har zuwa yau

Shekaru 32 da faruwar lamarin yau bincike yace ya gano mutanen 3 daga cikin wadanda suka kai harin a karkashin Abu Nidal, sakamakon shaidun da wasu boyayin mutane suka bayar, ga masu binciken da babban ofishin tsaron cikin gidan kasar faransa ke yi kan wannan dadden al’amari

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.