Isa ga babban shafi
Faransa

Kamfanin Faransa ya kafa gidauniya don samar da makamashi a Afrika

Wani Katafaren kamfanin wutar lantarkin Faransa da ake kira Schneider ya kafa wata gidauniya da za ta samarwa kasashen Afirka da ke kudu da sahara wutar lantarki saboda yadda yankunan ke fama da matsalar. Kamfanin da ke da cibiya a birnin Paris ya ce ganin yadda yanzu haka mutane miliyan 625 da ke zama a Yankin Afirka da ke kudu da sahara ke fama da rashin wutar lantarki ya zaburar da shi don ganin ya tallafa domin shawo kan matsalar.

Lantarki a garin Onicha na Najeriya
Lantarki a garin Onicha na Najeriya Annschunior
Talla

Kamfanin ya ce zai sanya kusan Dala miliyan 55 domin ganin an samarwa al’ummar da ke wannan yanki wuta saboda ganin yadda matsalar ta shafi rayuwar yau da kullum da kuma tattalin arzikin yankin.

Schneider ya ce burinsa sh ine ganin ya samarwa mutane miliyan guda wuta nan da shekarar ta 2020 a kanana da matsakaitan unguwannin da kuma sana’oinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.