Isa ga babban shafi
Ukraine

MDD tace an kashe fiye da mutane 6,000 a rikicin kasar Ukaraine

Majalisar Dinkin Duniya tace zuwa yanzu fiye da muten dubu 6 ne suka rasa ransu, tun bayan barkewar rikicin kasar Ukraine. Cikin wani rahoton da ya fitar yau Litinin, kwamtin kare hakkin dan Adam na Majalisar, ya bayyana takaici kan yadda ake salwantar da rayukan jama’a da dukiya a rikicin daya faro a watan Aprilun bara.Rahoton da kwamitin na kare hakkin dan Adam ya fitar a yau litinin, wanda shine na 9, a jerin rahotannin da yake fitarwa kan rikicin na Ukarine, ya nuna yadda aka salwantar da rayuka da dukiyoyi a kasar.Kwamishina mai kula da kare hakkin dan Adam na MDD Zeid Ra'ad Al Hussein, ya yi gargadi kan yuwuwar watsuwar rikicin fiye da yadda ake tunani.Kwamishinan ya yi kira ga bangarorin dake rikici da juna su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya ta birnin Minsk, su daina harba makaman roka ba ji ba gani, lamarin daya jefa fararen hula cikin halin ni ‘ya su.Lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rahoton a birnin Geneva, mataimakin Sakatare Janar na MDD mai kula da kare hakkin dan Adam Ivan Simonovic, yace kai wa fararen hula hari da gangan zai iya zama lafin yaki, in ya yawaita kuma cin zarafin bil Adama.Kalaman nasu na zuwa ne a daida lokacin da aka sami kwara kwaran zaman lafiya a gabashin Ukraine, lamarin daya sa ake fatan dukkan bangarorin zasu yi aiki da yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tangal tangal. 

Sakatare Janar na Majalisar Dinki duniya Ban Ki-moon,
Sakatare Janar na Majalisar Dinki duniya Ban Ki-moon, REUTERS/Faisal Al Nasser
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.