An zabi Erdogan a matsayin shugaban kasar Turkiyya
Firai Ministan kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya lashe zaben shugabancin kasar tun a zagayen farko da aka gudanar a ranar lahadin da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Erdogon, ya samu kashi 52% na kuri’un da aka jefa, inda yake shirin soma aiki a cikin makonni biyu masu zuwa. Zababben shugaban kasar dai ya bayyana cewa kasar za ta shiga wani sabon babi na ci gaba bayan da al’umma suka danka amanarsu a hannunsa.
Erdogon ya `zama Firai Minista ne tun a shekara ta 2003, kuma a yanzu zai karbi ragamar shugabancin kasar ne daga hannun Abdullah Gul wanda ya share tsawon shekaru 10 akan wannan matsayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu