Isa ga babban shafi
Turkiya

Erdogan ya yi wa gwamnatinsa garanbawul a Turkiya

Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi wa gwamnatinsa garanbawul sakamakon yadda batun rashawa ke neman haddasa rikicin siyasa a kasar. Wannan matakin na zuwa ne bayan Ministocinsa uku sun yi murabus.

Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Umit Bektas
Talla

Sabbin Ministoci 10 ne Firaministan ya bayyana sunayensu bayan ya gana da shugaban kasa Abdallah Gul.

Yanzu haka ‘Yan sanda sun kaddamar da binciken badakalar wasu kudade da aka karkatar da su zuwa kasar Iran da kuma zargin karbar cin hanci ga wasu ayyukan ci gaba a kasar.

Ministocin gwamnatin kasar Turkiya guda uku ne suka yi murabus daga aikinsu sanadiyar badakalar rashawa da shafi manyan Jami’an gwamnati da ‘yayansu, wanda hakan baraka ce ga gwamnatin Firaminista Tayyip Racep Erdogan.

A ranar Laraba ne Ministan Muhalli Erdogan Bayraktar ya ajiye aikinsa bayan tuni Ministan Tattalin arziki da na cikin gida suka bayyana yin murabus.

Bayan da Ministan Muhalli ya bayyana yin murabus, ya kuma yi kira ga Firaministan kasar Recep Tayyip Erdogan da ya bi sahunsu saboda binciken na rashawa da ake yi.

Wannan dai shi ne aka bayyana a matsayin babban kalubale da Erdogan ke fuskanta tsawon shekaru 11 da ya kwashe yana shugabancin Turkiya.

Akwai 'Ya'yan ministocin da ake zargi cikin mutane da dama da ake bincike game da zargin karbar cin hanci.

Erdogan dai ya danganta wannan al’amari a matsayin zagon kasa ga ci gaban tattalin arzikin Turkiya, amma masu lura da siyasar kasar na ganin hakan kuma baraka ce ga Jam’iyyarsa da kawayenta kafin gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Maris da kuma zaben shugaban kasa a watan Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.