Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa dan kabilar Roma

Shugaba Francois Hollande na Faransa, ya bayyana rashin jin dadinsa bayan dukan kawo wuka da wasu da ba asan ko su waye ba, suka yiwa wani matashi dan kabilar Rome inda suka barshi cikin halin rai kakwai mutu kakwai.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande a lokacin da yake ganawa da maneam labarai a birnin Brussels
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande a lokacin da yake ganawa da maneam labarai a birnin Brussels REUTERS/Laurent Dubrule
Talla

Wannan lamari ya jawo kakkausar suka daga kungiyoyin fararen hular kasar da dama, inda suka yi tir da cin zarafin da ake yiwa ‘yan kabilar ta Rome tsirari a kasar ta Faransa

Matashin dan shekaru 16 a duniya, wanda ake kira Darius, ya hadu da wannan hadari ne a ranar juma’ar da ta gabata a birnin Paris.

Shugaban Hollande dan jam’iyar gurguzu ta Socialist, ya ce hakan ya kaucewa duk wani tsari da aka kafa jamhuriyar Faransa da shi, ya kuma bukaci ganin jami’an tsaro sun bi duk hanyoyin da suka dace wajen gano wadanda suka aikata wannan cin zarafi.
 

A nasa bangaren Fira Ministan kasar, Manuel Valls, ya ce wannan lamari ba abin da za a amince da shi bane, inda ya bukaci gano wadanda suka aikata wannan aika aika ga matashin a cikin kankanin lokaci, domin gurfanar da su a gaban kotu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.