Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya bude bikin tunawa da Sojojin taron dangi

Shugaban Faransa Francois Hollande a yau Juma’a ya bude bikin cika shekaru Saba’in da Sojojin taron dangi suka yaki Sojojin Hitler a Faransa wanda ya hada kan Sojojin kasashe domin kawo karshen yakin duniya na biyu. Ana gudanar da bikin ne domin girmama Sojojin da suka mutu da fararen hula.

François Hollande na Faransa yan gaisawa da Vladimir Putin a harabar l'Elysée, fadar shugaban kasa a birnin Paris
François Hollande na Faransa yan gaisawa da Vladimir Putin a harabar l'Elysée, fadar shugaban kasa a birnin Paris REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth II da Barack Obama na Amurka da Vladimir Putin na Rasha suna cikin shugabanin da suka halarci bikin a arewacin Faransa domin tunawa tare da girmama Sojojin taron dangin da suka kwato Tsibirin Normandy daga Sojojin Nazi a shekara ta 1994.

Sojojin Taron dangi kimanin 156,000 ne suka dira a kasar Faransa a ranar 6 ga watan Juni na shekarar 1944 domin yakar dakarun Nazi.

Akwai tsoffin Sojoji ‘Yan mazan jiya kimanin 1,800 da za’a gudanar da bikin tare da su wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kwato Turai daga Ikon Nazi.

Yawancin ‘Yan Mazan jiyan sun haura shekaru 90, inda wannan taron mai dimbin tarihi da ake gudanarwa a Faransa zai kasance na karshe a gare su.

Wani batu da zai ja hankali a taron bikin shi ne ziyarar Shugaban Rasha Vladimir Putin wanda ke takun saka da kasashen Yammaci akan rikicin Ukraine.

A karon farko tun bayan da Rasha ta karbe Crimea, ana sa ran Shugaba Putin zai gana da manyan Shugabannin kasashen Turai David Cameron na Birtaniya da Francois Hollande na Faransa da kuma Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.