Wa’adin da Ukraine ta ba ‘Yan tawaye ya cika
Wa’adin da gwamnatin Ukraine ta ba sojojin sa-kai masu ra’ayin Rasha da suka karbe ikon gine-ginen gwamnati a gabacin kasar ya cika a yau Litinin, kuma babu wani alamu da ‘Yan tawayen suka nuna na bayar da hadin kai ga Ukraine.
Wallafawa ranar:
Tuni gwamnatin Ukraine tace zata yi amfani da karfin Soji ta murkushe su idan har ba su janye ba daga ginin Jami’an tsaro da suka karbe iko.
Kasashen Ukraine da Rasha na ci gaba da zargin juna da kokarin kaddamar da yaki a dai dai lokacin da dangantaka ke dada tsami a tsakaninsu bayan Rasha ta karbe Crimea daga Ukraine.
Rikicin Ukraine kuma ya janyo gurguncewar dangantaka tsakanin Rasha da kasashen yammaci da ke goyon bayan gwamnatin Ukraine da ke ra’ayinsu bayan hambarar da gwamnatin Viktor Yanukovych mai ra'ayin Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu