Isa ga babban shafi
Ukraine

Ukraine ta yi tayin afuwa ga mayaka masu ra'ayin Rasha

Shugaban rikon kwaryar kasar Ukraine ya yi tayin afuwa ga mayakan da suka mamaye gine ginen gwamnati masu ra'ayin Rasha idan har suka mika makamansu ko kuma a yi amfani da karfi a murkushe su.

Masu ra'ayin Rasha da suka mamaye gine ginen gwamnati a Donetsk na kasar Ukraine
Masu ra'ayin Rasha da suka mamaye gine ginen gwamnati a Donetsk na kasar Ukraine REUTERS/Maks Levin
Talla

Gwamnatin Ukraine ta ba Mayakan har zuwa Juma’a su fice daga gine ginen gwamanti da suka karbe iko a garin Lugansk da kuma Donetsk.

Mayakan da ke da’awar Rasha suna neman a gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a akan komawa ikon Rasha kamar yadda aka gudanar a yankin Crimea a watan jiya.

Amma Shugaban rikon kwarya na Ukraine Oleksandr Turchynoy mai ra’ayin Turai wanda ya gaji Viktor Yanukovich mai ra’ayin Rasha ya shaidawa zauren Majalisa cewa ana iya shawo kan Mayakan ta hanyar sulhu.

Wasu daga cikin ‘Yan Majalisar Ukraine yawancinsu masu ra’ayin Rasha sun gabatar da kudiri da ke neman a yi wa Mayakan Afuwa.

Tuni dai ‘Yan a waren a yankin Donetsk suka yi ikirarin kafa Jamhuriya mai cin gashin kanta tare da kira ga shugaban Rasha Vladimir Putin ya aika da dakaru a gabacin kasar domin kare kan iyakarsu da Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.