Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

Ukraine- Obama ya gana da Putin ta wayar talho

Kasar Rasha ta ce ba ta da niyyar mamaye sauran yankin kasar Ukraine, bayan da ta mallake yankin Crimea a ‘yan kwanakin da suka gabata. A cewar rahotanni, hukumomin kasar ta Rasha sun ce, sun fi son kasar ta Ukraine, ta ci gaba da zama a matsayin kasa mai zaman kanta, a wani mataki da Rashan ta ce tana ga hakan zai iya warware rikicin Ukraine.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Mihail Metzel/RIA Novosti/Kremlin
Talla

Wannan kalamai da suka fito daga kasar ta Rasha, na zuwa ne jim kadan bayan da Shugaba Vladimir Putin ya tattauna da takwaransa na Amurka, Barack Obama ta wayar talho, lamarin da masana siyasa a duniya ke cewa wata alamace dake nuna cewa an fara samo bakin zaren rikicin.

Yayin da ake shirin gudanar da zabe a kasar ta Ukraine nan da watan Mayu mai zuwa, dan takarar shugaban kasa, kuma shahararren dan wasan damben zamani, Vitali Klitschko, ya fice daga jerin ‘yan takarar kasar.

Dan shekaru 42, Klitschko ya janye ne domin ya marawa Petro Porosheknko baya, wanda ya shahara a fagen kasuwanci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.