Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Zai zama babban kuskure idan Rasha ta sake mamaye Ukraine- NATO

Kungiyar kasashen tsaro ta NATO ko kuma OTAN, ta gargadi kasar Rasha, da kada ta kuskura ta jawo ballewar wasu yankunan Gabashin Ukraine, bayan da ta karbe yankin Crimea a watan da ya gabata. 

Sakatare Janar na kungiyar NATO, Ander Fogh Rasmussen
Sakatare Janar na kungiyar NATO, Ander Fogh Rasmussen REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Tun bayan da Rasha ta karbe yankin Crimea daga kasar Ukraine, hukumomin wucin gadi a kasar ta Ukraine suka yi ta fama da bore, musamman ma a Gabashin kasar, inda mutanen yankin suke neman a jefa kuria’r raba gardama.

Lamarin da ya sa wasu masu bore suka mamaye wani ginin gwamnati a yankunan Donestk da Lugansk da kuma Kharkiv, da duk suke gabashin kasar ta Ukraine.

A kuma yau Talata ne shugaban kungiyar kasashen tsaro ta NATO ko kuma OTAN, Anders Fogh Rasmussen, ya ce babban kusukuren da Rasha za ta yi, shine ta sake mamaye wani yankin kasar.

Wannan gargadi na NATO na zuwa ne kwana daya, bayan da Amurka ta gargadi Rasha da ta daina daukan matakan da zai kara tsunduma kasar ta Ukraine cikin rikici, kamar irin mamaye kan iyakokin kasar da dakarunta suka yi.

Ita dai Amurka, tana dora laifin hargitsin dake faruwa a kasar ta Ukraine ne a kan Shugaban Rasha Vladimir Putin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.