EU
An bawa Kungiyar Tarayyar Turai Lambar Yabo ta zaman lafiya a hukumance
An bawa Kungiyar Tarayyar Turai ta EU Lambar Yabo ta wanzar da zaman lafiya a hukumance a yau Litinin, a wani yunkurin nuna kokarin da kungiyar ta yi na mayar da yankin daga fagen yaki zuwa nahiya mai zaman lafiya.
Wallafawa ranar:
Talla
Lambar yabon an ba da ita ne a idon wasu daga cikin shugabannin kungiyar, wadanda suka hada da Shugaban EU, Herman Van Rompuy, Shugaban Kwamitin Kungiyar, Jose Manuel Barroso da kuma shugaban ‘Yan majalisun kungiyar, Martin Schulz.
Shugaban kwamitin dake bada kyautar ne dan kasar Norway, Thorbjoern Jagland ya mika lambar yabon ga kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu