Isa ga babban shafi

Bill Gates da Dangote sun jaddada aniyar ci gaba da bunkasa sashen lafiyar Nijar

Shugaban Gidauniyar Gates Foundation, wato Bill Gates tare da takwaransa na Gidauniyar Dangote, Aliko Dangote sun sake jaddada aniyarsu ta aiki tare da hukumomin Jamhuriyar Nijar domin inganta ayyukan da su ke yi a kasar na bunkasa harkokin kula da lafiyar al’umma. 

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Bazoum Muhammad tare da Attajirin Amurka Bill Gates da kuma Attajirin Najeriya Aliko Dangote yayin ziyararsu a birnin Yamai fadar gwamnatin kasar.
Shugaban Jamhuriyyar Nijar Bazoum Muhammad tare da Attajirin Amurka Bill Gates da kuma Attajirin Najeriya Aliko Dangote yayin ziyararsu a birnin Yamai fadar gwamnatin kasar. © Niger Presidency
Talla

Bill Gates da Aliko Dangote sun bayyana aniyarsu ce yayin wata ganawar da suka yi da shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed a fadarsa da ke Birnin Yammai, inda suka tabo batutuwa da dama da suka hada da ci gaban al’ummar kasar. 

Bayan ganawar, Bill Gates ya bayyana cewar, sun mayar da hankali ne wajen tattauna irin ayyukan da suke yi a Nijar da suka shafi harkokin kula da lafiya da kuma ci gaba, yayin da suka jinjinawa gwamnatin Nijar akan irin matakan da take dauka a bangaren lafiya, musamman abinda ya shafi yaki da cutar pólio da kuma yiwa yara kanana rigakafi. 

Gates ya ce Gidauniyarsa da ta Dangote za su ci gaba da bada gudummawa wajen ganin Nijar ta samu nasarar shawo kan matsalolin da su ke fuskanta ta harkar kula da lafiya. 

Jami’in wanda ya yaba da hadin kan da su ke samu daga hukumomin Nijar, ya ce aikin da su ke yi a bangaren rigakafi na taimakawa wajen ceto dubban rayukan jama’a. 

Gates ya kuma bayyana cewar sun dauki alkawarin daukar matakin ganin na kawo karshen cutar polio a kasar baki daya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.