Isa ga babban shafi

Rayuwar dubban yara a Najeriya na cikin hatsari saboda rashin abinci - MSF

An samu adadin yaran da ba a taba ganin irinsu ba masu bukatar agajin ceton rai a cibiyoyin bayar da abinci mai gina jiki na kungiyar likitoci ta kasa da kasa wato Médecins Sans Frontières ko kuma Doctors Without Borders a Maiduguri, babban birnin jihar Bornon Najeriya.

Wani kwararren likita a Najeriya Japhet Udokwu, yayin duba lafiyar wasu kananan yara a garin Damaturu dake jihar Yobe.
Wani kwararren likita a Najeriya Japhet Udokwu, yayin duba lafiyar wasu kananan yara a garin Damaturu dake jihar Yobe. REUTERS - SEUN SANNI
Talla

Adadin bayanan wadanda aka samu tun daga farkon shekarar 2023 shi ne mafi girma da kungiyar MSF ta taba samu a jihar Borno a wannan lokacin da ake fama da yunwa, daidai lokacin da kayan abincin da aka girbe a baya suka kare inda matsalar rashin abinci mai gina jiki ta kai kololuwa.

MSF na gargadin bala'in da ke tafe idan ba a dauki matakin gaggawa ba.

"Karuwar adadin yaran da ke fama da tamowa yana bukatar rigakafin rashin abinci mai gina jiki da ayyukan jinya da za a habaka cikin gaggawa, domin kaucewa mummunar barazanar da ke tunkarar kananan yara," in ji babban wakilin MSF a Najeriya, Htet Aung Kyi.

Matsalar rashin abinci mai gina jiki ba sabon abu ba ne a Maiduguri, inda aka kwashe shekaru ana tashe-tashen hankula da rashin tsaro da suka haifar da munanan yanayin jin kai. Miliyoyin mutane ne suka yi gudun hijira daga gidajensu kuma a yanzu suna rayuwa cikin mawuyacin hali, tare da al'ummomin da suka karbi bakuncinsu, ko kuma a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Adadin majinyatan da MSF ta bawa kulawa saboda rashin abinci mai gina jiki ya karu a shekarar 2022, inda sama da yara 8,000 ke kwance a asibiti.

MSF ta ce, tallafin abinci ba shine kadai mafita ba, domin akwai bukatar kungiyoyin agaji su gaggata inganta shirin samar da abinci mai gina jiki, da kuma samar da karin gadaje a cibiyoyin kula da kananan yara da kef ama da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Daga farkon watan Janairu zuwa 20 ga Afrilu, 2023, an kwantar da yara 1,283 da ke fama da cutar tamowa a cibiyar MSF abin da ya zarce da 120 cikin 100 na adadin da aka samu a shekarar 2022, in ji kungiyar likitocin ta kasa da kasa.

A shekarar da ta gabata MSF ta ce  yara 147,860 suka yi fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a arewa maso yammacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.