Isa ga babban shafi

Rashin daukar mataki ya sa cutar kyandar biri ci gaba da barna a kasashe- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi kan yadda wasu kasashe ke tafiyar hawainiya a yaki da cutar kyandar biri ko kuma Monkeypox wadda ke ci gaba da fantsama sassa daban-daban.

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus. AP - Salvatore Di Nolfi
Talla

Wani rahoto da WHO ta fitar kan cutukan da ke bukatar kulawar gaggawa, ta ce har yanzu cutar ta kyandar biri na bukatar cikakkiyar kulawar gaggawa lura da yadda ta ke matsayin babban kalubalen lafiya a kasashe daban-daban.

Rahoton na WHO ya ce wajibi ne bangarorin lafiyar kasashe su yi hadaka wajen taimakekeniya don ganin an kawar da cutar daga ban kasa, musamman lura da yadda ta ke ci gaba da yaduwa cikin sauri.

A watan Yulin 2022 ne WHO ta ayyana cutar ta kyandar biri a matsayin babban kalubalen lafiya tare da gindaya matakan yaki da ita.

Shugaban hukumar ta WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa yanzu haka nau’in cutar ta kyandar biri an fi ganin bullarta a kasashen yankin Amurka yayinda ake ganin yadda ta ke kisa ba kakkautawa a kasashen Afrika da Turai.

A cewar sa lura da yanayin yadduwarta ta yadda mutum kan iya gogawa wani, akwai fargabar yiwuwar ta ci gaba da ta’azzara kamar yadda ake ganin karuwar masu cutar sida a ban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.