Isa ga babban shafi

WHO ta bukaci kasashe su farga bayan wani nau'in maganin tari ya kashe yara 300

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci kasashe su dauki matakin bayar da kariya ga yara kanana ta hanyar tantance nau’ikan magani da za a rika amfani da su tare da bayar da cikakken bayani kan duk wani nau’in magani da ya yi sanadiyyar kisa.

Nau'in maganin tari na Delkodin CC Cough Syrup da ya kashe yara a Gambia.
Nau'in maganin tari na Delkodin CC Cough Syrup da ya kashe yara a Gambia. IndiaMART
Talla

Wannan kira na WHO na zuwa ne bayan bayanan da ke nuna yadda kananan yara akalla 300 suka mutu a mabanbantan kasashe bayan amfani da wani nau’in maganin tari.

Hukumar WHO ta ce a watanni 4 da suka gabata ta samu rahotannin asarar rayuwa a kasashe daban-daban bayan shan magungunan tarin da ake sayarwa ta bayan fage wadanda aka sanyawa wasu sinadarai masu karfi da ke illa ga yara ciki har da diethylene glycol da kuma ethylene glycol.

A cewar hukumar gaurawa magungunan da wadannan sinadarai ya jefa rayukan tarin kananan yara a hadari ta yadda wasu suka mutu yayinda wasu suka samu illa ta din-din-din.

Hukumar ta ce zuwa yanzu kasashe 7 sun samu bullar nau’ikan magungunan tarin wadanda suka kashe yara fiye da 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.