Isa ga babban shafi

Yara dubu 40 na kamuwa da cutar Cancer a Najeriya duk shekara- bincike

Wasu alkaluma sun nuna yadda yara dubu 40 ke kamuwa da cutar Cancer ko suma sankara duk shekara a sassan Najeriya, wanda kuma bayanai ke cewa kaso mai yawa daga cikin wannan adadi basa samun kulawar da ta kamata wanda ke kaiwa ga rasa rayukansu.

Wata yarinya mai fama da cutar Cancer.
Wata yarinya mai fama da cutar Cancer. © 2013 Angela Chung/Human Rights Watch
Talla

Yayin wani taro da cibiyar kula da masu cutar Cancer ta Medicaid mallakin matar gwamnan jihar Kebbi a Abuja Hajiya Zainab-Shinkafi Bagudu ta ce abin takaici ne yadda dimbin rayuka ke salwanta duk shekara sanadiyyar cutar cancer.

Alkaluman da hukumar lafiyar ta fitar ta ce duk yaro 1 a cikin yara 285 na kamuwa da cutar Cancer kafin cika shekaru 20 a Duniya, inda a Najeriya cutar ta fi tsananta a tsakanin yaran da shekarunsu bai kai 15 ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce sabanin nau’in cutar ta Cancer da manya ke fama ita, galibin kananan yaran da kan harbu da cutar babu hakikanin abu guda da ke haddasa musu ita.

WHO ta ce ba kadai a Najeriya ba, cutar Cancer na zama kan gaba a sahun cutukan da ke lakume rayukan kananan yara, inda a duk shekara ta ke kashe dubu yara 160 ‘yan kasa da shekaru 15.

Shugaban sashen kula da kananan yara na babban asibitin Abuja, fadar gwamnatin Najeriya Dr Adewunmi Oyesakin ya ce hanya daya ta magance yawaitar mace-macen kananan yara sanadiyyar cutar ta cancer shi ne wayar da kai don daukar matakan kariya.

A cewar Dr Adewunmi akalla yara dubu dari biyar kan harbu da cutar Cancer tun daga karancin shekaru da kaso mai yawa a kasashen Afrika.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.