Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dunkin Duniya ta yi taron gaggawa kan Yemen

Kwamitin tsaro na majalisar dunkin Duniya ya gudanar da taro na gaggawa a kan atsalar yawan samun masu tsatssauran ra’ayi a Duniya, bayan kai harin da aka yi a kasar Yemen 

Talla

Idan ana iya tunawa a karshen Makon nan ne aka bada labarin kisan kusan mutane 150 a Masallaci, bayan da aka kai harin Bomb da kungiyar nan ta ISIS ta bayyana daukar alhaki.

Yanzu haka dai bayannai na nuna cewar kasar ta Yemen ta kasu kashi biyu, bangare daya wanda mabiya Shi’a ke jagoranta tare da samun taimakon kasar Iran, dayan kuma wanda ‘yan Sunni ke jagoranta.

Lalacewar sha’anin tsaro a kasar kuma ya hanawa shugaban kasar zama gidansa, da kuma fadar gwamnati, inda aka ce yanzu haka yana labe ne a wani wurin da ba’a bayyana a fili ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.