Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

MDD tace, Duniya na iya fadawa cikin matsalar ruwan sha

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi cewa, matukar ba’a samu sauye sauye ba, al-ummar duniya na iya fadawa cikin matsalar rashin ruwan sha, lamarin kuma, zai fi yin illa ga kasashe masu fama da zafi

Wasu Mutane a Yankin Asiya, na diban ruwan sha
Wasu Mutane a Yankin Asiya, na diban ruwan sha AFP
Talla

A wani rahotan da take fitarwa duk shekara, majalisar  tace, ta damu da yadda ake bannatar da ruwa, kuma in aka ci gaba a haka, za' a yi hasarar ruwan shan da ake dashi, da kashi 40 cikin 100, nan da shekara ta 2030.

Matukar ba’a dau matakan magance matsalar ba, yawan al-ummar dake cigaba da karuwa a kai a kai, na daya daga cikin abubuwan da zasu sa matsalar ta yi kamari, kamar yadda Majalisar ta bayyana kenan a cikin rahoton, inda ta kara da cewa, adadin al-ummar duniya a yanzu, ya kai biliyan 7.3 yayinda kuma, duk shekara ake samun karuwan mutane miliyan 80, lamarin da zai sa alkaluman su haura biliyan 9 nan da shekara ta 2050.

Majalisar tace, hakikanin gaskiya akwai ruwan da zai isar da bukatun kowa a duniya, abinda kawai ake bukata, shine a sauya yadda ake amfani da kuma rarraba shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.