Isa ga babban shafi

Facebook ya cire bidoyon wata likita da ta tallata maganin hydroxychloroquine

Wasu kafafen sada zumunta da muhara na intanet ciki har da Facebook da Twitter, sun cire wani bidiyo da ya dauki hankalin al’umma kwananan nan a shafukan na sada zumunta.

Kwayoyin maganin Hydroxychloroquine, da a baya ake amfani da shi wajen warkar da zazzabin malaria.
Kwayoyin maganin Hydroxychloroquine, da a baya ake amfani da shi wajen warkar da zazzabin malaria. GERARD JULIEN / AFP
Talla

Hoton bidiyon ya nuna wata likita 'yar Afirka, wanda wasu ke danganta ta da Najeriya mai suna Dr. Stella Emmanuel tana ikirarin cewa ta yi amfani da maganin hydroxychloroquine, zinc, da kuma Zithromax kan masu dauke da cutar korona a Amurka kuma ta warkar da sama da mutane 350, cikinsu har da tsoffi, da masu dauke da cutar hawan jini da tarin asthma.

Dr Stella wacce ma'aikaciyar lafiya ce a birnin Houston, na Amurka sai da tayi tattaki zuwa Washington DC, inda ta shaida wa manema labarai yadda tayi amfani da maganin wajen warkar da masu dauke da cutar ba tare da ko da mutun guda ya mutu a hannun ta ba.

An cire hoton bidiyon da ke nuna Likitar na bayani cikin fararen kaya na aikin likita kuma wasu mutane kewaye da ita, bayan da kusan mutane sama da miliyan 14 sun kalla, harma Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yada bidiyon a shafinsa na Periscope.

Daraktan sadarwa na Facebook Andy Stone ya bayyana ta shafinsa na Twitter cewa: sun cire bidiyon ne saboda ana yada labaran karya kan maganin cutar korona a cikinsa.

Shugaban Donald Trump ya taba bada fatawar amfani da maganin na hydroxychloroquine, a matsayin waraka ga cutar korona wanda ya tabbatar da cewar shidai yana amfani da shi, kafin ya sauya sheka zuwa maganin Remdesivir.

Yanzu haka adadin Mutanen dake mutuwa rana guda sakamakon kamuwa da cutar corona a Amurka ya yi tashin da ba’a taba gani ba tun watan Mayu, inda a cikin sa’oi 24 da suka gabata, mutane kusan 1,600 suka mutu.

Rahotanni sun ce an samu makwanni ana samun karuwar masu harbuwa da cutar a sassan kasar, kuma yanzu haka Jihar Florida ke sahun gaba wajen samun karuwar ta.

Yunkurin shugaba Donald Trump na samun nasarar zaben da za’ayi a watan Nuwamba na cigaba da dakushewa saboda yadda cutar ke dibar rayuka a kasar.

Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da dakatar da gwajin maganin na hydroxychloroquine tun a ranar 4 ga watan Tuni da cewar maganin bashi da tasiri kan cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.