Isa ga babban shafi

Mummunan harin bam a Cherniguiv a Ukraine bayan ganawar Putin da Janar dinsa

Rasha ta harba wani makami mai linzami zuwa cikin garin Cherniguiv da ke arewacin kasar Ukraine a yau Asabar.Rahotanni daga yankin na nuni cewa harin ya kashe akalla mutane 7 tare da raunata wasu 110, martanin Rasha da ke zuwa jim kadan bayan wani taron koli tsakanin Shugaba Vladimir Putin da manyan hafsan sojin Rasha.

Wani hari daga kasar Rasha a Ukraine
Wani hari daga kasar Rasha a Ukraine AP
Talla

Shugaba Putin ya samu ganawa da daya daga cikin janarori da ke kan iyakar kasar Ukraine. Sojojin Rasha sun kuma yi ikirarin cewa sun kakkabe sojojin Ukraine 150 da ke kokarin tsallakawa kogin Dnieper.

 Shugaban kasar Ukraine Volodomyr Zelensky ya koka a shafin Telegram cewa "Wani makami mai linzami na Rasha ya tarwatse a tsakiyar gari Cherniguiv.

Rasha ra kai makami mai linzami a Ukraine
Rasha ra kai makami mai linzami a Ukraine via REUTERS - STATE EMERGENCY SERVICE OF UKRAI

Shugaban na Ukraine ya bayyana cewa Akalla mutane bakwai ne suka mutu yayin da wasu 110 suka jikkata a harin na Rasha.

Sakamakon da mukaddashin magajin garin birnin ya fitar a yau asabar,jami’in ya karasa da cewa harin bama-baman ya baiwa mutane mamaki a wani birni da aka kubuta a cikin 'yan watannin nan daga manyan hare-hare bayan da sojojin Rasha suka yi masa kawanya a wani dan lokaci a farkon mamayar a watan Fabrairun 2022.

Shugaban kasar Ukraine
Shugaban kasar Ukraine AFP - HANDOUT

Harin na zuwa kasa da kwana daya bayan da Amurka a jiya Juma'a ta amince da kasashen Denmark da Netherlands da su aike da jiragen yakin F-16 zuwa Ukraine. Har ila yau, harin ya faru ne a lokacin da Volodymyr Zelensky ya ziyarci Sweden, abokiyar kyiv da ke son shiga NATO duk da mummunar adawa daga Moscow.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.