Isa ga babban shafi
Amurka-HRW

China da Cuba yakamata a bincika kan nuna wariya maimakon Amurka- Pompeo

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana matakin Hukumar kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya kan yin tir da halin nuna wariyar da bakar fata ke fuskanta a Amurkan da kuma kafa kwamitin bincike kan batun a matsayin abin da ya wuce gona da iri, tare da yunkurin kambama batun.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo Mark Wilson/Getty Images/AFP
Talla

A cewar Pompeo maimakon bata lokacin wajen bincike ko kuma caccakar halin da bakar fata ke ciki a Amurka, kamata ya yi hukumar ta mayar da hankali wajen bincike kan tsagwaron wariyar da ake nunawa bakar fatar a kasashen China da Cuba wadanda ke matsayin mambobin hukumar.

Kalaman na Pompeo na zuwa bayan matakin hukumar na kada kuri’a da ya bata damar umarnin gudanar da bincike kan korafe-korafen nuna wariyar da kaswashen Afrika suka shigar mata biyo bayan kisan George Floyd da ‘yansandan suka yi a Minneapolis.

Zaman hukumar a yammacin jiya juma’a dai ya dakatar da Afrikan daga gudanar da bincike da kanta inda maimakon haka hukumar karkashin jagorancin Michelle Bachelet ta dauki aniyar gudanar da bincike.

Tun shekaru 2 da suka gabata ne dai Amurkan ta fice daga hukumar mai mambobib 47 saboda abinda ta kira sukar matakan wariyar da Israila ke nunawa Falasdinawa.

A cewar Mike Pompeo daga matakin da gwamnatin Amurkan ta dauka kan jami’an da ke da hannu a kisan George Floyd duniya ta gane cewa babu gurbin nuna wariya a cikin kasar, haka zalika bakar fata na da cikakkiyar dama kamar kowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.