Isa ga babban shafi

Amurka na shirin maido da dangantakar tsaro da Jamhuriyar Nijar

Amurka ta kudiri aniyar maido da dangantakar bunkasa kasa da Jamhuriyar Nijar matsawar ta dauki matakin dawo da mulkin dimokaradiyya, kamar yadda wata jami’ar diflomasiyyar kasar ta bayyana, jim kadan bayan ganawa da jagororin sojin da suka kifar da gwamnatin kasar a watan Yuli.

U.S. President Joe Biden holds an event about American retirement economics in the State Dining Room at the White House in Washington, U.S., October 31, 2023.
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - LEAH MILLIS
Talla

Mataimakiyar Sakataren harkokin Afrika, Molly Phee ta ce ta gana da manyan ministocin gwamnatin sojin Nijar, inda ta kwarfafa musu gwiwa su  sanar da jadawalin mika mulki ga gwamnatin farar hula nan ba da jimawa  ba.

Phee ta shaida wa wani taron manema labarai cewa ta  bayyana wa jagororin sojin Nijar kudirin Amurka na maido da dangantakar tsaro da bunkasa kasa idan har masu mulkin suka yi abin da ya dace.

Nijar ta kasance abokiyar hulda mai mahimmanci ga Amurka  a yakin da take da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, wadanda suka yi sanadin mutuwar dubban mutane a yankin Sahel na nahiyar Afrika.

Kamar Faransa da sauran kasashen yammacin Turai, Amurka  ta yanke duk wani tallafi da take bai wa Nijar biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, sai dai ba ta janye dakarunta  daga kasar ba, abin da ke nuni da cewa ta bar wata kafa ta dangantaka.

Gwamnatin sojin Nijar ta sallami dakarun Faransa daga kasar, kana ta yanke dangantakar tsaro da Tarayyar  Turai bayan juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.