Isa ga babban shafi

An samu raguwar adadin 'yan jarida da ke mutuwa a bakin aiki - RSF

Adadin ‘yan jarida da aka kashe yayin gudanar da aikinsu  ya ragu a wannan shekarar, duk kuwa da yadda aka samu mutuwar wasu a Zirin Gaza watanni biyu da suka wuce, kamar yadda kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta The Reporters Without Borders ta bayyana a Alhamis din nan.

Christophe Deloire, babban sakataren kungiyar Reporters Without Borders.
Christophe Deloire, babban sakataren kungiyar Reporters Without Borders. © RFI
Talla

Rahoton na RSF ya bayyana cewa a cikin watanni 11 na farkon shekarar 2023, ‘yan jarida 45 ne suka  mutu a bakin aikinsu, kasa da 61 da suka mutu a sshekarar da ta gabata.

Wannan ne adadi mafi karanci tun bayan da ‘yan jarida 33 suka mutu a shekarar 2002, kuma hakan ya faru saboda raguwar mutuwar ‘yan jarida da aka samu a yankin Latin Amurka.

A yayin da ‘yan jarida 63 ne suka mutu a Gabas ta Tsakiya tun da aka fara yakin da ya barke a ranar 7 ga watan Oktoba tsakanin Isra’ila da Hamas, 17 ne kawai suka shiga kundin RSF na wadanda suka mutu a bakin aiki.

Babban sakataren kungiyar RSF, Christophe Deloire  ya ce abinn da ake la’akari da shi a wannan rahoto shi ne raguwar adadin ‘yan jarida da suke mutuwa a bakin aikinsu, wanda  akwai tazara tsakanin adadin wannan shekarar da na shekarun 2012 da 2013, inda 140 ne aka kashe sakamakon yakin Syria da Iraq.

Ya kara da cewa kungiyoyi masu zaman kansu ne suka yi hobbasa har ka samu raguwar mutuwar ‘yan jarida a bakin aiki, da kuma irin taka tsantsan da ‘yan jaridar kan su suka nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.