'Yan jaridar Kamaru 2 sun bukaci kariya daga barazanar kisan da ake musu
Wasu ‘yan jarida biyu a Kamaru, sun bukaci gwamnatin kasar da ta basu kariya, sakamakon barazanar kashe su da wani magajin gari ke yi, biyo bayan binciken kwakwaf din da suke gudanarwar akan zarginsa da hannu a a wata badakalar cin hanci da rashawa a wasu manyan ayyukan shimfida tituna da ya bayar.
Wallafawa ranar:
‘Yan jaridar da ake zargin Magajin garin Maroua Sali Babani da yi wa barazana dai sun hada da Aminou Alioum wakilin kafar yada labaran Cchannnel 2 International da ke Douala, sai kuma Ousman Alhaji Boubakari.
‘Yan jaridun biyu sun ce an sha kiran wayoyinsu a lokuta da dama, tare da yi wa rayuwarsu barazana, muddin basu daina watsa rahotannin da ke caccakar magajin garin da suke bincike kan ayyukansa ba.
Wannan barazana na zuwa ne kasa da watanni uku, bayan kashe wasu manema labarai da aka yi cikin watan Janairun da ya gabata a kasar ta Kamaru, sakamakon ficen da suka yi wajen kkokarin bankado laifukan cin hanci da rashawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu