Isa ga babban shafi
Iran-Nukilya

Hukumar Sa'ido kan Nukiliya ta cimma matsaya da Iran

Shugaban hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, an cimma matsaya ta wucin-gadi" na tsawon watanni uku da zai baiwa hukumar damar ci gaba da sanya ido kan Iran, duk da cewa matakin sahalewar zai takaita daga ranar Talata.

Shugaban Hukumar dake sa'ido kan mukamashin Nukilya ta duniya Rafael Grossi
Shugaban Hukumar dake sa'ido kan mukamashin Nukilya ta duniya Rafael Grossi Reuters
Talla

Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya da ke Vienna, Rafael Grossi wanda ya shaida hakan ga manema labarai, bayan tattaunawa da shugabannin Iran, yace, matakin nada matukar tasiri wajen dinke barakar da ake da shi yanzu haka.

Grossi ya bayyana ci gaban ne, bayan shafe kwanaki biyu yana ziyara a Iran, inda ya tattauna da shugabannin Iran kan shirinta na nukiliya, sa’o’i gabannin cikar wa’adin da ta diba na takaitawa hukumar, gudanar da bincike, ciki harda ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif, da kuma shugaban hukumar sarrafa makamashi na kasar Ali Akbar Salehi.

Tun a watan Disamba ne, Majalisar dokokin Iran wacce ke da rinjayen masu ra'ayin rikau ta zartar da doka inda ta bukaci kasar ta dakatar da masu binciken hukumar idan har Amurka ta gaza cire mata takunkuman da ta kakaba mata, dokar za ta fara aiki daga gobe Talata.

Grossi baiyi cikakken bayani game da ayyukan da hukumar ta IAEA, ba za ta iya yi ba, amma ya tabbatar da cewa ba za a rage yawan jami’an da ke cikin kasar ta Iran ba, kuma za a ci gaba da binciken gaggawa a karkashin tsarin na wucin gadi.

Matakin da ke zuwa yayin da Amurka da Tarayyar Turai suka kara azama a kokarinsu na ceto yarjejeniyar nukiliyar 2015, wacce ke daf da rugujewa tun bayan da tsohon shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga cikinta.

Muddin wa’adin ya cika ba tare da Amurka ta janye takunkuman ba, Iran za ta kara bijirewa yarjejeniyar ta da manyan kasashe kan shirin ta na nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.