Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dunkin Duniya ta karbi Rahoton Kwamitinta kan Yakin Falesdinu

Kwamitin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa dan gudanar da bincike kan yakin da aka kwashe kwanaki 50 anayi a Gaza ya bukaci Karin lokaci dan gabatar da rahotan sa saboda aje aikin da shugaban sa William Schabas yayi

Des enfants jouent dans les ruines de bâtiments dans le quartier d'al-Shejaiya, à Gaza City, le 26 février 2015.
Des enfants jouent dans les ruines de bâtiments dans le quartier d'al-Shejaiya, à Gaza City, le 26 février 2015. FP PHOTO / MOHAMMED ABED
Talla

Da dai an shirya kwamitin zai gabatar da rahotan sa ne ranar 23 ga watan nan ne, sai kuma kwamitin ya rubutawa hukumar kare hakkin Bil’adama ta Majalisar dunkin Duniya bukatar a bashi Karin lokaci har zuwa watan Yuni mai zuwa.

Israila dai na adawa da aikin kwamitin, bisa wasu dalilan da bata fitar a fili ba, koda yake masu lura da al’amurra na ganin cewar sakamakon Kwamitin ba zai yiwa kasar ta Isra’ila dadi ba.

Idan ana iya tunawa a yakin da kasar Isra’ila ta tafka da kungiyar Hamas a baya, Isra’ilar ta yita kaucewa kiraye-kirayen da kassahen Duniya ke mata na dakatar da kisan bayin Allah amma Isra’ilar na ta sa Kafa tana fatali da kiran.

Isra’ila dai na kokarin hanawa kungiyar Hamas tasiri ne a yankin gabas ta tsakiya, domin kar ta yi karfin da za ta iya yakar kasar ta Isra’ila a cikin dan kankanen lokaci.

Sai dai duk da kisan da Isra’ilar ke yiwa Falasdinawa a Gaza, akasarin mutanen Gaza basu da tsoron kasar ta Isra’ila a Zukatansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.