Libya
Libya na neman izinin sayo makamai
Kasar Libya ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta ba ta damar sayen makamai don magance barazanar kungiyoyin ‘yan ta’addan da suka addabi kasar. Jakadan Libya a Majalisar, Ibrahim Dabbash, ya gabatarwa kwamitin sulhun bukatunsu don ganin an gaggauta amincewa da ita domin ceto Libya daga hannun ‘yan ina-da-kisan da yanzu haka ke cin karen su babu babbaka.
Wallafawa ranar:
Talla
Bukatun na Libya sun hada da sayen jiragen yaki 14 da ake kira MIG Fighter jets, helicoftoci 7 da tankuna yaki 150 da kuma motocin sulke masu dauke da bindigogi 150 da na’urar harba gurneti 10,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu