Isa ga babban shafi
Iran

An koma tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran a Vienna

Ministan harkokin wajen kasar, Mohammed Javad Zarif ya bayayna haka, yayin ganawar da suka yi da Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman Lakhdar Brahimi, wanda ke ziyarar kwanaki uku a kasar ta Iran.

Cathrine Ashton da kuma ministan wajen Iran
Cathrine Ashton da kuma ministan wajen Iran Reuters/Heinz-Peter Bader
Talla

Da ma dai Majalisar dunkin Duniya ce ta bukaci Iran da ta sa Baki domin kawo karshen fadan na kasar Siriya da aka dade ana yi tsakanin ‘yan tawaye masu samun taimakon kasashen Turai da kuma Sojin Gwamnati masu kariya ga shugaba Bashar al-Assad.

A baya dai Majalisar dunkin Duniyar ta bada Kai Bori yah au ne, ga bukatar ‘yan tawaye da suka kememe akan gayyatar da Majalisar ta dunkin Duniya ta yiwa Iran a taron tattaunawa karo na 2, taron da aka kammala ba tare da cimma wata matsaya ba.

‘Yan tawayen dai sun tsaya ne akan batun sauya Gwamnatin shugaba Assad, a yayinda bangaren gwamnatin kasar ya ki amincewar da matakin na ‘yan tawaye, tare da bayyana bukatar a kai karshen masu tada Kayar Baya.

Taron dai ya kai mai shiga tsakani na Majalisar dunkin Duniya Lakdar Brahimi ga neman ahuwar Duniya akan yanda bangarorin 2 suka bata lokaci basu yi gaba ba, basu kuma yi baya ba.

Ita dai Iran ta ki amincewa da bukatar kafa gwamnatin rikon kwarya a Syria, inda take bukatar ganin anyi zabe dan baiwa al’ummar kasar damar zabin abinda suke so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.