Lokaci ya yi da zamu biya diyar cinikin bayi da mukayi - Shugaban Portugal
Shugaban Portugal Marcelo Rebelo de Sousa, ya ce kasarsa ce ke da alhakin aikata laifukan bautarwa da aka yi a lokacin mulkin mallaka, don haka ya ce akwai bukatar a biya diyyar laifukan da aka aikata.
Wallafawa ranar:
Akalla ‘yan Afirka miliyan 12 da dubu dari 5 ne aka yi safaransu ta hanyar jiragen ruwa zuwa Turai, inda aka sayar da su a matsayin bayi.
Daga cikin wancan adadi, Portugal kadai ta fitar da ‘yan Afrika miliyan 6 da ta sayar dasu a matsayin bayi, lamarin da ya sanyata zama kasar da ta fi yawan cinikayyar bayi a nahiyar Turai.
A lokacin da shugaba Rebelo de Sousa ke ganawa da manem alabarai a jiya Talata, ya ce kasarsa ce ke da alhakin duk wani lafin bautarwar da aka samu a baya, don haka ya ce lokaci ya yi da ya kamata su biya diyar laifukan da aka aikata.
Ko a shekarar da ta gabata, sai da shugaban na Portugal ya nemi afuwa kan tsarin bautar da suka yi da kuma mulkin mallaka, duk da cewa a jiya Talata ya ce daukar alhakin laifin ne yafi muhimmanci.
Fafutukar da ake yi na ganin an biya diyar laifukan bautarwar da aka yi a baya na samun karbuwa a duniya, ciki kuwa harda kokarin samar da kotu ta musamman da za ta yi shari’a kan lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu