Isa ga babban shafi

Duniya na bikin ranar tunawa da kawo karshen cinikin Bayi

Kowacce ranar 23 ga watan Agusta ita ce ranar tunawa da cinikin bayi ta Duniya, da kuma matakin da aka dauka don kawo karshen wannan safara da masana ke bayyanawa a matsayin daya daga cikin abubuwa na kunya mafi muni da suka taba faruwa a tarihin duniya.

A kowacce ranar 23 ga watan Agusta ne ake bikin tunawa da ranar kawo karshen cinikin bayin.
A kowacce ranar 23 ga watan Agusta ne ake bikin tunawa da ranar kawo karshen cinikin bayin. AFP - NICOLAS TUCAT
Talla

Cinikin bayi, fatauci ne da aka gudanar daruruwan shekaru da suka gabata, kafin manyan kasashen duniya su zauna tare da kulla yarjejeniyar kawo karshensa a farkon karni na 20, to sai dai kafin lokacin alkalumma sun tabbatar da cewa an bautar da milyoyin mutane a sassa daban na duniya.

Duk da cewa matsala ce da ta shafi yankuna da dama a wancan lokaci, to amma bayanai na nuni da cewa nahiyar Afirka ce ta fi kowane sashe na duniya cutuwa daga wannan safara, sakamakon yadda aka kwashe milyoyin matasa majiya karfi zuwa Turai da Amurka don bautar da su ta hanyar noma da kuma masana’antunsu.

A irin wannan rana ta 23 ga watan Agustan kowace shekara, ana gudanar da turuka don tunawa da zagayowar wannan rana musamman a Afirka da kuma yankin Caribbien, yayin da masu fafutuka ke amfani da wannan rana don jaddada bukatar ganin cewa an biya diyya saboda illolin wannan safara.

Har zuwa yau dai ana ci gaba da bayyana bauta a matsayin salon tauye hakkin bil’adama mafi muni da aka taba aikatawa a tarihin duniya, kuma ko a cikin kwanakin da suka gabata sai da shugaban Ghana Nana-Akuffo Ado ya bukaci a biya Afirka diyya saboda wannan ta’annati da duniya ta yi ma ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.