Isa ga babban shafi

Ya kamata a biya diyyar bayin da aka kwasa daga Afirka - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce lokaci yayi da kasashen Turai za su biya diyya ga bayin da aka diba daga nahiyar Afirka shekaru aru-aru da suka gabata ga gwamnatocin kasashen su.

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres kenan.
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres kenan. REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

Majalisar na bayyana hakan ne, yayin taron da aka fara a ranar Talata, kan al'ummar Afirka da kuma halin da nahiyar ke ciki, inda ta bukaci karin kudade domin tallafawa ayyukanta.

Sama da karni hudu aka dauka ana diban bayi daga Afirka da yawansu ya kai miliyan 12.5, inda ake safarar su ta jiragen ruwa, yayin da ake hada-hadar su a nahiyar Turai.

Wadanda suka tsira daga mummunar doguwar tafiyar da ake daukar dubban kilomita sun kare da yin aiki ne a gonaki, musamman a cikin Amurka, Brazil da kuma yankin Karebiya, bugu da kari akwai wadanda suke cin gajiyar aikin bautar da suka yi a wancan lokaci.

A cikin wani sakon bidiyo da ya gabatar a wajen bude taro da aka shirya kan al'ummar Afirka a birnin Geneva, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya jaddada cewa, matsalar wariyar launin fata da ake ci gaba da fama da ita a halin yanzu, ta ta'allaka ne a kan bauta da mulkin mallaka na tsawon shekaru aru-aru da bakar fata suka fuskanta.

Babban magatakardar na MDD, ya ce ya kamata a dauki mataki ainun kan wannan matsala, idan har an shirya kawo karshen matsalar wariyar launin fata.

Antonio Guterres, ya ci gaba da cewa, akwai wadanda suka fuskanci ukuba a hannun turawan da suka yiwa aikin bauta, inda suka kare rayuwar su a cikin mummunan yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.