Isa ga babban shafi

Mutane 10 sun mutu a hadarin jiragen sama masu saukar ungulu a Malaysia

Mutane 10 suka mutu a lokacin da wasu jirage masu saukar ungulu na sojojin Malaysia biyu sun yi karo da juna, yayin wani atisaye da suke yi a yau Talata.

Yadda jami'an bada agaji ke kokarin gano wadanda suka rasa ransu a hadarin jiragen sama masu saukar ungulu a Malaysia.
Yadda jami'an bada agaji ke kokarin gano wadanda suka rasa ransu a hadarin jiragen sama masu saukar ungulu a Malaysia. via REUTERS - FIRE AND RESCUE DEPARTMENT OF MA
Talla

Babban jami’in gudanarwa na hukumar kwana-kwana da aikin ceto ta kasar, Suhaimy Mohamad Suhail ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Firaministan kasar Anwar Ibhrahim ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin da ya bayyana a matsayin mai tada hankali, inda ya ce za a gudanar da bincike don gano musabbabin faruwansa.

An gayamin cewar ma’aikatar kula da harkokin tsaro za ta gudanar da bincike, musammanma rundunar sojojin ruwa ta kasa TLDM, don gano musabbabin farun hadarin.

Ba kasafai aka cika samun aukuwar hadarin jiagen sama masu saukar ungulu a kasasshen da ke shiyar Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya ba.

Amma a watan da ya gabata, wani jirgin sama mai saukar ungulu na jami’an da ke tsaron gabar ruwan Malaysia yayi hadari a mashigar Malacca, duk da dai ba a samu asarar rai ba.

Haka nan a shekarar 2016, akwai mataimakin ministan kasar da ya rasa ransa a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Sarawak da ke kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.