Isa ga babban shafi

Yau ake cika kwanaki 200 da barkewar rikicin Hamas da Isra'ila

A yau Talata ce yakin Isra'ila da Hamas ya cika kwanaki 200 da faroshi, lamarin da ke haifar da fargaba game da yadda Isra'ila ke ci gaba da mamaye yankin Gaza, a kokarin da ta ce ta ke yi don ta kubutar da mutanenta da Hamas ta yi garkuwa da su.

Yadda hare-haren Isra'ila suka lalata gine-ginen yankin Gaza a cikin kwanaki dari biyu da faro rikicinsu da Hamas.
Yadda hare-haren Isra'ila suka lalata gine-ginen yankin Gaza a cikin kwanaki dari biyu da faro rikicinsu da Hamas. REUTERS - Dawoud Abu Alkas
Talla

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ce a cikin daren jiya, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare a garuruwan Al-Tuffah da Shajaiya da kuma Zeitun da ke makwabtaka da Gaza.

Haka nan antajin karar ababen fashewa a garin Khan Yunis da ke kudancin Gaza sannan sojojin Isra’ila sun kai hari da jiragen sama da makaman atilari kusa da sansanonin ‘yan gudun hijira na Bureij da kuma Nuseirat.

Daya daga cikin jiragen yakin Isra'ila.
Daya daga cikin jiragen yakin Isra'ila. AP - Leo Correa

Sojojin Isra’ilan sun ce sun samu nasarar lalata wasu cibiyoyin Hamas da ke yankin.

Asalin rikicin

Wannan yaki ya samo asali ne bayan da mayakan Hamas suka kai hari cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban bara, inda suka kashe kimanin mutane dubu daya da dari 2 tare da yin garkuwa da wasu sama kimanin dari 250.

Daga nan ne Isra’ila ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya da nufin kubutar da mutanenta da aka yi garkuwa da su.

A sanadiyar hare-haren Isra’ila, kawo yanzu ma’aikatar kula da lafiyar ta yankin Falasdinu ta ce kimanin Falasdinawa dubu 35 ne suka mutu wasu kimanin dubu 78 suka jikkata, yawancin su kuma mata ne da kananan yara.

Gawarwakin wasu daga cikin Falasdinawa da suka rasa rayukansu a Gaza.
Gawarwakin wasu daga cikin Falasdinawa da suka rasa rayukansu a Gaza. AFP - -

Halin da iyalan wadanda Hamas ta yi garkuwa da su ke ciki

Tun bayan garkuwa da mutanen da Hamas ta yi a cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, iyalan wadanda aka yi garkuwa da ‘yan uwansu sun matsawa gwamnatin kasar lamba wajen ganin na bukubar da iyalansu.

A cewar wata sanarwa da Dalit Shtivi mahaifiyar Idan Shtivi da aka yi garkuwa da shi a wajen bikin kalwankuwa a ranar 7 ga watan Oktoba, ta ce har yanzu tana cikin jimamin batan dan nata.

Akwai ciwo, ba zan iya kwatanta irin kunar da nake ji ba.

A wani sakon karfafa gwiwa da firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya aikewa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, ya sha alwashin ganin gwamnatinsa ta kubutar da al’ummarta.

Matsayar kasashen kan hare-haren Isra’ila

Bayan sanarwar da Isra’ila ta yi na kai farmaki yankin Rafah ta kasa, da kusan mutane miliyan biyu da dubu dari 4 ke samun mafata a cikinsa, kasashen da dama da kungiyoyi sun matsawa Isra’ila lamba don ta kare hakkin hakkin fararen da ke wajen..

Kungiyar kasashen masu karfin tattalin arzki na 7 na daga cikin wadanda basa goyon bayan wannan hari.

Barazanar yaduwar rikicin a yankin gabas ta tsakiya

Kwana daya da kai farmakin Hamas cikin Isra’ila, ita ma kungiyar Hezbollah ta fara kai hari cikin Isra’ala daga Lebanon.

Haka nan ita ma kungiyar mayakan Houthi ta kasar Yemen, ta kaddamar da hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila a tekun Maliya.

Irin wadan nan matakai ne dai ya sanya kasashe da kungiyoyi yin kira don kaucewa yaduwar rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai duk da kiraye-kirayen da aka yi, sai dai Isra’ila ta kai hari ofishin jakadanci  Iran da ke Syria, Wanda yayi sanadiyar sojojin rundunar juyin juya hali.

Jagoran addini na Iran Ayatullah Ali Khamenei, a gaban gawarwakin sojojin rundunar juyin juya halin kasar da harin Isra'ila ya kashe a Syria.
Jagoran addini na Iran Ayatullah Ali Khamenei, a gaban gawarwakin sojojin rundunar juyin juya halin kasar da harin Isra'ila ya kashe a Syria. via REUTERS - Wana News Agency

Faruwar hakan ke da wuya, Iran ta dauki matakin kai harin ramuwar gayya cikin Isra’ila ta hanyar harba makaman nukiya da jirage marsa matuna sama da dari 3, lamarin da ya sanya sabunta kiraye-kirayen kai zuciya nesa kan wannan rikici.

Rashin amincewa da hare-haren Isra'ila

Bayan kaddamar da hare-haren Isra'ila a yankin Gaza, zanga-zanga ta barke a wasu kasashe ciki har da na Turai, inda suke suna goyon bayansu ga Falasdinawa da kuma nuna rashin amincewa da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Ko a farkon wannan makon sai da aka gudanar da zanga-zanga a Amurka na ganin Isra'ila ta kawo karshen hare-haren da take kaiwa Falasdinawa.

Daya daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zanga a birnin New York na kasar Amurka a ranar 22 ga watan Afelerun 2024.
Daya daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zanga a birnin New York na kasar Amurka a ranar 22 ga watan Afelerun 2024. REUTERS - Eduardo Munoz

Karancin kayan agaji a Gaza

Wannan rikici dai ya sanya mutane da dama rasa ransu sakamakon karancin kayan kula da lafiya da kuma na abinci a yankin Gaza.

Hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu UNRWA, ta bayyana fargabartar barkewar yunwa a yankin Gaza.

Sakamakon karancin abincin da aka fuskanta a yankin na Gaza, a cikin watannin da suka gabata rahotanni sun nuna yadda wasu Faladinawa suka fara cin ciyawa.

Gawar daya daga cikin jami'an kungiyar WCK.
Gawar daya daga cikin jami'an kungiyar WCK. AP - Abdel Kareem Hana

Haka nan, rikicin ya yi sanadiyar da dama daga cikin jami'an bada agaji a yankin Gaza, na baya-bayannan shi harin da Isra'ila ta kaiwa ayarin motocin jami'an kungiyar World Central Ketchen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.