Isa ga babban shafi

Birnin Edinburgh ya nemi gafarar 'yan Afirka akan cinikin bayi

Birnin Edinburgh dake kasar Scotland, ya nemi gafara akan rawar da ya taka wajen bautar da bayin da aka dauko daga kasashen Afirka da kuma mulkin mallakar da aka yiwa yankunan su a karkashin mulkin Birtaniya.

Birtaniya dai ta yiwa kasashen da dama na Afirka mulkin mallaka
Birtaniya dai ta yiwa kasashen da dama na Afirka mulkin mallaka © Henry P. Moore / Library of Congress / Wikimedia public domain
Talla

Shugaban mulkin Birnin Robert Aldridge ya gabatar da neman gafarar lokacin bude taron majalisar mulkin birnin, inda ya bayyana cewar a matsayinsa na shugaba, yana neman gafarar duk wadanda suka fuskanci azabtarwa ko kuma jefa su cikin mummunar yanayi sakamakon mulkin mallakar ko kuma bauta.

Aldridge yace illar mulkin mallaka da kuma bauta sun mamaye sassan birnin da gine ginen dake ciki da hukumominsu da kuma harsashin da aka kafa Edinburgh da shi.

Shugaban yace babu yadda zasu musanta irin ribar da birnin ya samu sakamakon shekarun da aka kwashe ana bautar da jama’a musamman wadanda suka fito daga kasashen Afirka.

Neman gafarar na zuwa ne bayan da wani bincike da aka gudanar ya danganta birnin da hannu dumu dumu wajen cinikin bayi da kuma mulkin mallaka.

Daya daga cikin shawarar da wadanda suka yi nazari akan rahotan binciken suka bayar, itace ta neman gafarar a bainar jama’a akan rawar da Edinburgh ya taka a mulkin mallaka da kuma cinikin bayi da akayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.