Isa ga babban shafi

Yammacin Afirka ya kasance babbar hanyar safarar miyagun kwayoyi a duniya - MDD

Wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ya nuna cewa, yankin Sahel mai fama da rikici ya zama wata babbar hanya mai tasirin gaske wajen safarar miyagun kwayoyi, abin da ke ci gaba da yin kamari, saboda gazawar gwamnatoci da kuma kungiyoyin masu dauke da makamai da ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Yadda wani soja ke duba jakar da ke dauke da hodar iblis, ranar 21 ga Maris, 2021, a cikin wani jirgi mai saukar ungulu. Lokacin sojojin ruwan Faransa sun kwace tan shida na hodar iblis da darajarsu ta kai Yuro biliyan 1 daga wani jirgin ruwan dakon kaya da ya taso daga Kudancin Amurka zuwa gabar tekun yammacin Afirka.
Yadda wani soja ke duba jakar da ke dauke da hodar iblis, ranar 21 ga Maris, 2021, a cikin wani jirgi mai saukar ungulu. Lokacin sojojin ruwan Faransa sun kwace tan shida na hodar iblis da darajarsu ta kai Yuro biliyan 1 daga wani jirgin ruwan dakon kaya da ya taso daga Kudancin Amurka zuwa gabar tekun yammacin Afirka. © Corentin Charles / AP
Talla

Rahoton da ofishin da ke yaki da ta’ammali da muggan kwayoyi na Majalisar ya fitar ya ce, a shekarar 2022, an kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1,466 a kasashen Mali, Chadi, Burkina Faso da Nijar, abin da ke nuna cewa abin ya yi kamari idan aka kwatanta da kilogiram 13 da aka cafke a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2020.

Rahoton ya ce an fi kama masu safarar hodar iblis, maimakon wadanda ke dakon tabar wiwi a yankin na Sahel.

Binciken ya zo ne a daidai lokacin da kasar Senegal da ke kan iyaka da yankin Sahel ta sanar da cewa, an samu nasarar kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1,137, da aka yi kiyasin kudinta ya kai dala miliyan 146 a gabashin kasar.

Yankin Sahel dai na kudu da Hamadar Sahara wato ya yi iyaka da Tekun Atlantika zuwa yankin kasashen Larabawa, abin da ke ganin shi yasa ya zama babbar hanyar safarar hodar iblis din da ake dauka daga Kudancin Amurka zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya.

Yadda jami’an tsaron gabar ruwan Spain suka gano wani jirgin ruwa mai dauke da sama da tan hudu na hodar iblis a tsibirin Canary, ranar 15 ga Fabrairu, 2024.
Yadda jami’an tsaron gabar ruwan Spain suka gano wani jirgin ruwa mai dauke da sama da tan hudu na hodar iblis a tsibirin Canary, ranar 15 ga Fabrairu, 2024. AFP - HANDOUT

Wakilin sashen yaki da safarar miyagun kwayoyi na MDD, Amado Philip de Andres, a yammaci da tsakiyar Afira, ya ce safarar muggan kwayoyin da ake yi a yankin na ci gaba da haifar da illa ga harkokin kiwon lafiya, tare da cewa ana samun karuwar hada-hadar kayayyakin maye a nahiyar ta Afirka.

Wani abin takaicin da ke faruwa a cewar rahoton, shine musayar tabar wiwi samfurin kasar Morocco kai tsaye da hodar iblis din da ta fito daga Kudancin Amurka, musamman a yankin Afirka ta Yamma.

Wannan sabon salon da ya faro tun daga shekarar 2020, MDD ta ce an samar da shi ne domin kayyade farashin muggan kwayoyin a tsakanin nahiyoyin, abin da ke kara yawaitar abubuwan mayen da ake safarar su ta kan tudu kafin su shiga jiragen ruwa, musamman a yankunan Sahel da ke fama da rikici.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa, cin hanci da rashawa da halasta kudaden haram ne ke haifar da fataucin muggan kwayoyi, sannan kuma bisa kamen da ake yi da kuma bincike ya nuna cewa jiga-jigan ‘yan siyasa, shugabannin al'umma da shugabannin kungiyoyin masu dauke da makamai suna taka rawa sosai, wajen safarar miyagun kwayoyin da ake yi a yankin na Sahel.

Wakilin babban sakataren MDD a yammacin Afirka, Leonardo Santos Simão, ya ce dole ne kasashen yankin Sahel tare da kasashen duniya su hada kai wajen daukar matakan gaggawa, idan har 123357ana son wargaza hanyoyin safarar miyagun kwayoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.