Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta yi maraba da ziyarar babbar jami’ar Diplomasiyyar Turai Catherine Ashton

Hukumomi a kasar Iran sun yi maraba da ziyarar da babbar Jami’ar harkokin Diplomasiyyara kasashen Turai Catherine Ashton ta kai masu a birnin Tehran karsen Satin da ya gabata, duk da cewar ta sha suka kan batun kare hakkin bil’adama da ta fito da shi a ziyarar tata

Catherine Ashton a kasar Iran
Catherine Ashton a kasar Iran deccanchronicle.com
Talla

A ranar Lahadin da ta gabata dai Ashton ta samu ganawa da shugabannin kasar ta Iran da suka hada da Shugaban kasar Hassan Rouhani da kuma Ministan kula da harkokin wajen Iran Mohammad Java Zarif.

Kasashen Trawa dai a kwanan nan na ta biyar Iran da batun kulla kakkarfar alaka a tsakaninsu, kuma kamar yanda Ofishin shugaban kasar ya sanar, Ashton ta gabatar da sakon fatan Alkhairi daga kasashen kungiyar tarayyar Turai 28 zuwa ga Hassan Rouhanni.

Kasashen dai na kamun-Kafa ne ta hanyar ita Catherine Ashton dangane da yarjejeniyar da ke kumshe a tattaunawar da ke tsakanin Iran da manyan kassahen Duniya masu fada a ji da suka hada da Amurka da Faransa da China da Jamus da Rasha domin ganin cewar Iran bata karkacewa yarjejeniyar da aka yi tun daga farko ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.