Isa ga babban shafi
Faransa-Iran-Amurka

An cimma matsaya kan shirin Nukiliyan Iran

Yau Alhamis, Kasar Iran ta cimma matsaya da manyan kasashen duniya, kan jadawali da hanyoyin da za a bi, don samar da yarjejeniya kan shirin Iran din kan sinadarin nukiliya. Bayan yau na birnin Viennan kasar Austria, ministar harkokin wajen kungiyar taraiyyar Turai Catherine Aston tace a ranar 17 ga wata mai zuwa, za a ci gaba da tattaunawar da ake yi don cimma matsaya.Ashton ta kara da cewa taron, da aka yi tsakani Iran da kasashen Amurka, China, Rasha, Britaniya, Faransa da Jamus, da kuma aka shafe kwanaki 3 ana tattaunawa ya taimaka matuka, don an cimma yarjejeniyar da ake bukata.Ana fatan zaman zai tabbatar da muhimmiyar yarjejeniyar da aka kulla a birnin Geneva kasar Switzerland a cikin watan Nuwamban bara.Yarjejeniyar ta Watan Nuwamba, da ta fara aiki a ranar 20 ga wata Junairun wanan shekarar, ta bukaci Iran ta dakatar da wasu shirye shiryenta na Nukilya, yayin da za a sassauta mata wasu daga cikin takunkumin da aka kakaba mata.Kawararru sun ce wannan zai kunshi rufe cibiyar Fordo da ke karkashin kasa, rage yawan sinadarin Uraniyum da ake hakowa, canza aikin wata cibiyar da ke Arak, da barin kwararru na MDD su shiga kasar don sa ido. 

Wasu daga cikin wakilan da suka halarci taron na Vienna
Wasu daga cikin wakilan da suka halarci taron na Vienna Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.