Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka ta yi barazanar karfafa takunkumi kan Iran

Kasar Amurka ta yi barazanar karfafa wa kasar Iran takunkumi domin yin gargadi musamman ga wakilan kasashe irin su Faransa da suka kai ziyara Tehran domin kulla huldar kasuwanci.Sama da wakilai 100 ne daga Faransa da suka kunshi har da wakilan kamfanonin kasar irinsu Total da Peugeot, suka kai ziyara birnin Tehran a ranar Litinin domin kulla kawancen kasuwanci da kasar.Wannan kuma bayan an sassutawa kasar Iran jerin takunkumin da kasahen Turai da Amurka suka kakkaba mata bayan cim ma yarjejeniya game da shirin ta na Nukiliya.Mataimakin Shugaban kungiyar kwadago, da ke cikin tawagar da suka kai ziyarar yace sun je ne domin duba yadda kasuwarsu zata karbu a kasar ta Iran, bayan janye takunkumin na kasashen Turai. Amma kasar Amurka ta kalubalanci ziyarar domin a cewar sakataren harakokin waje John Kerry, har yanzu akwai takunkumin da ba a janye wa Iran ba.Amurka tace takunkumin da aka sassauta wa Iran na wuccin gadi ce, kuma yarjejeniyar da aka kulla akan dakatar da ayyukan kera Nukiliya ce za ta nuna matakin da za a dauka a gaba.Baya ga Faransa dai akwai tawagar kasar Turkiya da ta kai ziyara kasar ta Iran, domin karfafa huldar kasuwanci. 

Shugaban Amurka, Barack Obama
Shugaban Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.