Isa ga babban shafi
Iran-Syria-MDD

Iran ta nemi kasashen duniya su zuba jari a kasar

Shugaban kasar Iran Hasan Rohani, ya yi kiran kasashen duniya da su zuba jari a kasarsa, Kafin ya yi tsokaci kan yanda za’a warware rikicin kasar Syriya.Rohani ya fadi hakanne yau Alhamis, lokacin da yake jawabi a gaban zauren taron tattalin ariziki na kasashen Duniya, da ake yi a birnin Davos na kasar Swaziland.Cikin dogon jawabin da ya gabatar kan karfin tattalin arzikin kasarsa, Hasan Rohani ya nemi kasashen dake makwabtaka da Iran da kuma na tarayyar Turai da ma sauran kasashen duniya, cewa kofar kasar Iran abude take garesu domin zuba jari da kuma hada hadar tattalin arziki a kasar IranRohani dake jawabi a gaban shugabanin kasashen da na kamfanoni hade da masana tattalin arziki na duniya, sama da dubu 1500 da suka hadu a birnin Davos, ya kwadaitar da su kan irin dimbin albarkatun makamashi da Allah ya horewa kasar ta Iran, bayan da a makon da ya gabata aka dage wasu jerin takunkuman kariyar tattalin arzikin da aka kakaba mata a bayaA lokacin da yake tsokaci kan rikicin kasar Syria kuma, shugaba Rohani yace hanya guda ce zata iya kawo karshen yakin basasar dake ci gaba da lakume rayukan jama’a, ita ce ta shirya sahihin zaben gaskiya da adalci a kasar ta SyriyaRohani yace babu wani bangare ko kuma wata kasa mai karfi daga wajen kasar ta Syria da zasu ari bakin al’ummar kasar su ci masu albasa, a matasayin ta na kasa mai cikakken yanci, inda ya kara da cewa makomar Syriya ta dogara ne akan zabin al’ummarta. 

Hassan Rohani, a yayin taron tattalin arziki da ake yi a birnin Davos
Hassan Rohani, a yayin taron tattalin arziki da ake yi a birnin Davos REUTERS/Denis Balibouse
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.