Isa ga babban shafi
Amurka-Iran-Isra'ila

Netanyahu ya soki kasashen duniya kan kasar Iran

Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya soki kasashen duniya kan abinda ya kira munafincin su kan kasar Iran, yayin da yake bayyana makaman da kasar ta aike da su zuwa Yankin Gaza.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Sebastian Scheiner/Pool
Talla

Netanyahu wanda yake jawabi a gaban makaman, ya ce abin bakin ciki ne yadda duniya ta ki amincewa da barazanar Iran, ganin yadda take ci gaba da taimakawa ayyukan ta’addanci a duniya.

Israila na zargin Iran da aikewa da makamai wa kungiyar Hamas a Yankin Gaza yayin da take ci gaba da nuna adawa da zaman sasantawar da ake da Iran da manyan kasashen duniya game da makamashin nukiliyanta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.