Isa ga babban shafi
MDD

Mambobin MDD sun soki Amurka akan Cuba

Akalla kasashe 188 ne suka marawa Majalisar Dinkin Duniya baya wajen yin Allah wadai da takunkuman da kasar Amurka ta kakabawa Cuba, lamarin da Cuba ta kwashe shekaru hamsin tana fuskanta.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

Kasar ta Amurka ta samu goyon bayan kasar Isra’ila ne kawai a zauren majalisar wacce ke da mambobi 193 wajen kin amincewa da wannan mataki da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka a wannan shekara.

A bara dai kasashe biyu ne suka mara mata baya wanda hakan ke nufin kasar ta Amurka ta kara samun koma baya wajen goyon bayan da ta ke samu akan lamarin.

Rahotanni sun ce har kasashen China da Iran dake kokarin kyautata dangantakarsu da Amurka ba su goyi bayan ta ba, a lamarin na ci gaba da kakaba tukunkumai a kan Cuba.

A yanzu haka kasar ta Cuba yi hasarar kudi triliyan 1.1 na dalar Amurka saboda takunkuman a cewar Minisitan Harkokin kasashen wajen Cuba, lamarin da har ila yau ya dakile irin tallafin da kasar ke samu wajen yaki da cutar kanjamau ko kuma SIDA.

Sai dai Amurkan ta ce matsalolin dake addabar kasar ta Cuba basu da alaka da takunkuman da kasar ke fuskanta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.