Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Sakataren MDD Ban Ki Moon ya gana da manyan kasashen Duniya kan Siriya.

Sakataren Majalisar dunkin Duniya ban Ki moon ya gana da Jakadun kasashen Burtaniya da China da Faransa da Rasha da Amurka a kan batun amfani da Makami mai Guba a Siriya bayan da ya yanke ziyarar da yake a Nahiyar Turai.

Ban Ki-moon da Barack Obam
Ban Ki-moon da Barack Obam blogs.cfr.org
Talla

Ban Ki moon dai yayita kashedi ga shugaban kasar Amurka Barack Obam da sauran shugabannin kasashen Duniya akan kar su kai farmakin Soji a kasar Siriya har sai Jami’an majalisar dunkin Duniya sun kammala aikin su a can.

Jakadan Burtaniya a Majalisar dunkin Duniya Mark Lyall Grant yace zasu duba binciken da jami’an majalisar dunkin Duniya suka gudanar sannan su tattauna sosai akan matsalar ta kasar Siriya.

Masu binciken Makami mai Guba na Majalisar dunkin Duniya dai na shirin barin kasar Siriya ne a ranar Assabar, sannan su mikawa Sakataren na Majalisar dunkin Duniyar cikkakkun bayannai akan wanan batu.

Kasar Amurka da masu goyon bayan ta dai sun matsu basu kai farmaki a Sirya ba, a yayinda kasashen Rasha da China ke ci gaba da kekasa kasa akan wanan matsakin da Turawan yammacin Duniya ke shirin dauka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.