Isa ga babban shafi
Najeriya

Matasan Kiristoci da Musulmin Arewacin Najeriya sun nemi hadin kan juna

Shugabanin matasan Kiristoci da Musulmi daga yankin Arewa maso gabacin Najeriya, sun gudanar da wani taron fahimtar juna don shawo kan matsalolin da ke addabar yankin musamman barazanar tsaro da kuma rikicin Addini da Kabilinaci ganin Yadda ake ci gaba da samun hare hare da kuma daukar fansa a Yankin.

Kasuwar  Abubakar Gumi ta cika da mutane a Garin Kaduna bayan Gwamnatin ta sassuta dokar hana Fita daga sa'oi 24 saboda rikicin da ya lakume rayukan mutane sama da 90.
Kasuwar Abubakar Gumi ta cika da mutane a Garin Kaduna bayan Gwamnatin ta sassuta dokar hana Fita daga sa'oi 24 saboda rikicin da ya lakume rayukan mutane sama da 90. REUTERS/Stringer
Talla

Taron ya mayar da hankali ne game da hare haren daukar Fansa da aka kai a garuruwan Bauchi da Kaduna da Zaria bayan tashin bama bamai a Biranen. Taron kuma ya yi la’akari da dangantakar kud-da-kud da ke tsakanin Mabiya Kirista da musulmi a iyali daya.

04:20

Rahoton Shehu Saulawa

Shehu Saulawa

Akwai musayar Litattafai da Kasidu da aka yi a Taron game da Abubuwan da Addinan Biyu suka kunsa, musamman kan batutuwan da suka shafi makwabtaka da kare hakkin Juna.

Shugaban Matasan kiristoci a shiyar Arewa maso Gabacin Najeriya yace akwai Ziyara da suka samu daga matasan Musulmi wadanda kuma suka ba Kiristocin wasu Littafai guda biyu da ke bayani game da addinin Musulunci.

A cewar Mista Musa Littafan sun taimaka sosai ga wasu Fastoci wajen fahimtar ma’anar addinin Musulunci musamman hakkin makwabtaka a Musulunci.

A nasa Bangaren, Dakta Abdurrashid Adbulgani Shugaban hadin gwiwar matasan Musulmin Arewa yace sun yi haka ne domin ilmantar da Kiristoci ma’anar Musulunci domin koda wani musulmi ya yi kuskure, kiristocin ba za su yi tunanin Musulunci ne ya karantar da shi ba.

Taron ya nemi kai zuciya nesa tsakanin kiristoci da musulmi tare da bukatar Gwamnati yin adalci wajen hukunta wadanda aka kama da haddasa rikici.

A karshen makon jiya ne aka samu tashin bama bamai a Kaduna da harbe harben Bindiga a Damaturu, al’amarin da yasa gwamnatocin Jahohin suka saka dokar hana Fita ta sa’o’I Ashirin da Hudu.

An samu hasarar rayuka da dama sakamakon hare haren a Biranen Kaduna da Damaturu.

Al’umar Jihar Kaduna na ci gaba da bayyana halin da suka samu kansu, sakamakon tashin hankalin da aka samu a Jihar, wanda ya lakume rayukan mutane da dama, daga bisani kuma aka kakaba ma su dokar hana fita na sa’oi 24 kusan mako guda ke nan.

Amma gwamnatin Jihar tace, ta rage wa’adin dokar, dan ganin mutanen Jihar sun numfasa, kamar yadda Gwamnan Jihar, Patrick Ibrahim Yakowa ya shaida wa Rfi Hausa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.