Isa ga babban shafi
Najeriya

Rikici ya lafa a Kaduna bayan mutuwar mutane 101 a Najeriya

An samu barkewar rikici a wasu unguwannin Kaduna a daren jiya Laraba tsakanin mabiya addinin kirista da Musulmi duk da dokar hana fita ta sa’o’I 24 da aka sa a Jahar bayan kai wasu hare haren bama bamai da rikicin kabilanci da suka yi sanadiyar hasarar rayuka 101.

Wani Sojan Najeriya yana tafiya a dai dai wurin da bom ya tashi a jahar Kaduna Najeriya
Wani Sojan Najeriya yana tafiya a dai dai wurin da bom ya tashi a jahar Kaduna Najeriya Reuters/Stringer
Talla

Akwai Rahotanni daga ‘Yan Sanda da Mazauna kaduna wadanda suka ce an yi fito-na-fito tsakanin Musulmi da kirista tun a daren Laraba cikin dokar hana Fita a unguwannin Badarawa da Malali da Barnawa da Hayin Gada.

Rahotanni sun ce an samu kone konen Tayu a saman Tituna tare da kona shagunan mutane.

Tun a ranar Lahadi ne Najeriya ke cin wuta a Kaduna da Damaturu inda gwamnatocin Jahohin Kaduna da Yobe suka sa dokar hana fita.

Wasu al’ummar Damaturu sun ce suna cikin mawuyacin halin rashin Abinci tun a ranar Litinin da aka kafa dokar hana fita bayan musayar wuta tsakanin ‘Yan Bindiga da Jami’an tsaro.

Yanzu haka an samu lafawar harbe harbe a garin Damaturu, amma Kwamishinan ‘Yan Sandan Jahar Yobe Patrick Egbuniwe yace dokar hana fita za ta ci gaba da aiki bayan samun mutuwar mutane 40.

Daga Fadar Vatican, Fafaroma Benedict na XVI ya yi kiran kawo karshen Zubar da jini a Najeriya tare da neman bangarorin da rikicin kasar ya shafa gujewa daukar Fansa.

Sai dai Shugaban Kungiyar Kristocin Najeriya, Fasto Ayo Orijitsafor, ya bayyana bacin ransa da hare haren da ake ci gaba da kai wa mabiyansu, inda ya ke cewa, idan suka fara ramako, ba zai haifar da abu mai kyau ba.

Yanzu haka Gwamnatin Jonathan tana fuskantar kalubale saboda halin da Najeriya ta shiga.

Tuni Jam’iyyar adawa ta ACN a Najeriya, ta bayyana damuwa da bacin rai game da tafiyar shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zuwa wani taron kula da muhalli a kasar Brazil, a dai dai lokacin da wasu Jahohin kasar ke cin wuta. Kuma wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Majalisar wakilan kasar ta nemi bayani daga Shugaban game da halin da Najeriya ta shiga.

Ministan yada Labaran Najeriya Labaran Maku ya mayar da martani wanda yace a jingine Siyasa a gefe domin fuskantar halin da Najeriya ta shiga.

A cewar Mista Maku, Shugaba Jonathan ya tafi aiki ne a Brazil domin halartar babban Taron da ya shafi rayuwar al’ummar Duniya, yana mai cewa idan akwai wani abu da Najeriya ke bukata akwai mataimakin Shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.